ABNA24: Kafafen watsa labarun duniya da dama na cikin gida da kuma waje, sun nuna hoton shugaban kasar ta Najeriya Muhammadu Buhari da takunkumin rufe bakin wanda ya sanya a karon farko tun bullar corona.
Wannan dai ita ce tafiya ta farko zuwa kasar waje da shugaban kasa ta Najeriya ya yi a cikin watannin da corona ta bulla a duniya.
Ziyarar ta Muhammad Buhari zuwa Mali tana a karkashin kokarin da kasashen yammacin Afirka su ke yi ne na warware takaddamar siyasar kasar ta Mali.
Shugabannin kasashen Senegal, da Ivory-Coast sun riga yi shugaban na Najeriya isa birnin Bamako.
Waadanda su ka biyo bayansa kuwa su ne Shugabannin kasashen Ghana, Nana Addo Dankwa Akufo-Addo sai kuma Muhammadu Issufu na Nijar.
342/